Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon minista da wanda ya wakilci jihar Taraba, Malam Muazu Sambo.
An gudanar da taron ne jim kadan gabanin bude taron kwamitin tsaro na kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
Sambo ya maye gurbin tsohon Ministan wutar lantarki, Mamman Sale, daga Taraba, an mayar da shi ma’aikatar ayyuka da gidaje a matsayin karamin ministan ayyuka da gidaje.
A halin yanzu dai shugaba Buhari ya na jagorantar taron majalisar tsaro na kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Wadanda su ka halarci taron na tsaro sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da ministocin harkokin ‘yan sanda da shari’a da kuma na tsaro, harkokin cikin gida da na kasashen waje.
Sauran sun hada da hafsoshin tsaro, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya; Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba; Babban Darakta Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje, Yusuf Bichi da kuma Darakta Janar na NIA, Abubakar Rufa’i.