A ranar Litinin ne wa’adin da wata kotu ta bai wa kamfanin Facebook na biyar tarar dala miliyan 290 bisa samun sa da laifin karya dokoki.
A watan Yulin 2024 ne dai kotun ta umarci kafamin da ya biya tarar bayan samun shi da laifin taka dokokin da suka jiɓanci gasa da tallan haja da kuma na bayanan sirri.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko kamfanin na Meta zai biya wannan tara da kuma matakin da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka idan kamfanin ya gaza bin umarnin kotun.
A watan Mayu ne kamfanin na Meta mamallakin Facebook ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya bisa abin da ya bayyana da tarar da ta wuce hankali.
Wani rahoto ya nuna cewa al’ummar Najeriya ka iya rasa damar ci gaba da hulɗa da shafukan Facebook da Instagram idan dai har kamfanin na Meta ya aiwatar da barazanar da ya yi na rufe ayyukan nasa a ƙasar.