fidelitybank

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Date:

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya domin jana’izar marigayi, fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijo, Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina.

Marigayi Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, a ranar Asabar yana da shekara 94.

Tawagar ta bar Najeriya da yammacin Lahadi, inda ta isa Madina da safiyar Litinin.

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata da dai sauran su.

Akwai kuma manyan malamai a cikin tawagar da suka haɗa da sheikh Aminu Daurawa da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad.

the sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Pillars ta dauki yan wasa guda biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta tabbatar da...

An cafke ‘yan Daba 28 a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu...

Na yafe wa Buhari duk abun da ya yi min – Buba Galadima

Buba Galadima, wanda tsohon abokin marigayi Muhammadu Buhari ne...

Shugabannin Afrika za su halarci jana’izar Buhari

Ana sa ran wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka...

Yadda ake shirye-shiryen jana’izar Buhari a Daura

A yanzu haka dai alumma na ta tururuwa domin...

Shettima ya yi wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari ta’aziyya a Landan

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi wa wasu...

Indiya na jimamin mutuwar Buhari – Modi

Firaministan India Narendra Modi, ya shiga jerin shugabanni da...

Kungiyar Gwamnoni sun bayar da hutu kan mutuwar Buhari

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu...

Tinubu ya bayar da hutu don yin ta’azziyar Buhari

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan...

Shettima ya isa Landan domin dawo da gawar marigayi Muhammadu Buhari

A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim...

Najeriya ta yi rashin Buhari – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rasuwar tsohon...

Tabbas Buhari mutum ne mai kyakyawan halaye mai kishin kasa – IBB

Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya, Janar Ibrahim Babangida,...
X whatsapp