fidelitybank

Kirsimeti: Gwamnati za ta yi jigilar  jirgin kasa kyauta na tsawon kwana 11

Date:

Gwamnatin tarayya ta sanar da fara jigilar ‘yan Najeriya ta jirgin kasa kyauta tun daga ranar 24 ga watan Disamba har zuwa 4 ga watan Janairu na shekarar 2022.

Manajan darakta na hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Fidet Okhiria, ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.

Ya ce: “Shawarar da a ka yanke tare da hadin gwiwar ma’aikatar sufuri, ita ce ta saukaka zirga-zirgar ‘yan kasa a lokacin bikin Kirsimitei na yuletide.

“Wannan shi ne domin taimakawa sauƙaƙe farashin sufuri da baiwa ƴan ƙasa damar motsawa cikin sauƙi, domin jin daɗin lokacin bukukuwa.

“Duk da haka a na shawartar fasinjoji da su tabbatar sun samu tikitin su daga wuraren da su ka dace ba tare da farashi ba, don ba su damar shiga da shiga cikin jiragen.

“An kuma umarci dukkan fasinjoji da su kiyaye da kuma yin biyayya ga dokokin Korona ta hanyar sanya abin rufe baki da hanci da tsaftace hannu”. Inji Fidet.

Ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da jiragen kasa a wannan lokacin.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp