fidelitybank

Gwamnatin Kebbi ta yi hadin gwiwa da Likitocin kasa da kasa

Date:

Kungiyar likitoci mai zaman kanta ba tare da iyaka ba ta kasa da kasa ta kasar Faransa, (Doctors without Borders) ta ce a shirye ta ke ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Kebbi, domin isar da ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar jihar.

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ne ya karbi bakwancin tawagar karkashin jagorancin shugaban tawagar, Dr Shaukat Muttaqi a gidan gwamnati dake Birnin Kebbi.

A lokacin da ya ke karbar tawagar,  a madadin gwamnan, shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu, ya yi maraba da likitocin tare da bayyana farin cikinsa dangane da shirye-shiryen sanya hannu kan yarjejeniyar (MOU) da hadin gwiwa da gwamnati.

Ya kuma tabbatar wa da tawagar cewa, gwamnatin jihar Kebbi za ta samar da yanayi mai kyau, domin gudanar da aikin yadda ya kamata wajen samun kyakkyawan aiki.

Shugaban tawagar, Dr. Shaukat Muttaqi ya bayyana cewa, makasudun ziyarar ta su ita ce, tattauna muhimman ayyukan da suka kiwon lafiya da shirin samar da abinci mai gina jiki da kuma kula da matsalolin al’umm a jihar Kebbi.

A cewarsa, kungiyar Doctors without Borders ta dukufa wajen samar da ayyukan jinya kyauta ga al’ummar jihar Kebbi a shirinta na watanni shida na farko tare da fatan cimma yarjejeniya da ma’aikatar lafiya da jihar Kebbi, domin fara ayyuka cikin gaggawa.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

ÆŠaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla ÆŠanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An É—age jana’izar Aminu ÆŠantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da É—age jana'izar fitaccen É—ankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp