fidelitybank

Daliban Kano 3 sun shiga jerin sahun wadanda a ka fi kafa hujja da su a fanin kimiyya na duniya

Date:

Wasu dalibai 3 da toshon gwamnatin, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ta dauki nauyin karatun su, Drs Aliyu Isa Aliyu da Tukur Abdulkadir Sulaiman, da kuma Abdullahi Yusuf, sun shiga cikin jerin sahun gaba na cikin kashi 2 na masana kimiyya wadan da a ka fi nema a duniya.

Jerin sunayen su, wanda a ka buga a watan Agusta 2021, a cikin ƙungiyar masu bincike ne suka shirya wanda, Farfesa John Loannidis na Jami’ar Stanford, California da ke Amurka.

Jerin ya haɗa da masu bincike sama da 100,000 waɗanda a ka zaɓa tsakanin masana kimiyya sama da miliyan 8 a cikin fagagen kimiyya 22 da ƙananan 176 a duk faɗin duniya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, an haifi Dr. Abdullahi Yusuf a karamar hukumar Dala a jihar Kano. Ya kammala karatunsa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano a shekarar 2010. Ya samu digirin digirgir (Ph.D) a Applied Mathematics daga jami’ar Firat University, Elazig ta kasar Turkiyya a 2019.

An haifi Dr. Tukur Abdulkadir Sulaiman a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano. Ya kammala karatunsa a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 2009. Ya samu digirin digirgir (Ph.D). wanda ya yi karatu a fannin lisafi na Applied Mathematics a jami’ar Firat, Elazig, Turkiyy a 2019.

An haifi Dr. Aliyu Isa Aliyu a karamar hukumar Bichi ta jihar Kano. Ya kammala karatunsa a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 2009. Ya samu digirin digirgir (Ph.D) na Applied Mathematics a jami’ar Firat Elazig, Turkiyya a 2018.

Matasan malaman uku na daga cikin wadanda su ka ci gajiyar tallafin karatu na kasashen waje na gwamnatin jihar Kano a zamanin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso daga 2011 zuwa 2014. An dauki nauyin karatunsu a shekarar 2012 domin yin digiri na biyu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jordan da ke Irbid ta kasar Jordan.

Mutanen uku a halin yanzu su na aiki da Sashen Lissafi na Jami’ar Tarayya Dutse da ke Jigawa a Najeriya.

 

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa ƴar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar Ɗangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp