Shugaba Biden ya ce, Amurka za ta tura sojoji domin kare Taiwan idan da China za ta mamaye tsibirin.
Wannan shi ne wani ƙwaƙƙwaran bayani da yayi abin da ya kawo karshen tirka tirka da Amurkan ta jima tana yi akan tsibirin tsawon shekaru.
Da yake jawabi a yayin wata ziyara da ya kai Japan, Mr Biden ya ce Amurka za ta ci gaba da yarda akan manufar China na kasancewa kasa guda.
To amma idan har gwamnatin Chinan ta kawo batun mamaye Taiwan, to kuwa hakan zai kawo babbar matsala a gaba dayan yankin, kuma Amurkan da kawayenta ba za su bari akan ya faru ba bisa la’akari da bin da ya faru a Ukraine.
Da yake goyon bayan shugaba Biden a wajen wani taron manema labarai, fira ministan Japan Fumio Kishida ya ce dole a rinka bibyar duk wasu huldodin China musamman na sojojin ruwanta a yankin Taiwan.
Ya ce dangane da China, za mu rinka bibiyar duk wasu harkokin sojin ruwanta da kuma huldar hadin gwiwarta da Rasha.
Muna matukar sukar duk wani yunkuri na kawo wata matsala a yankunan tekun China na Gabashi da Kudanci.
Tuni mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, ya ce kasarsu ta yi amfani da wadannan kalamai yana mai kara da cewa dama Taiwan wani muhimmin yanki ne na China. In ji BBC.