Hisbah ta tabbatar da cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba, tare da gannin ta yi dukkan mai yuwa, domin hana film dinnan da ya ƙunshi kalaman batsa mai suna Makaranta.
Hukumar Hisbah ta jihir ta yi tir da Allah wadarai da film din nan mai Suna makaranta Wanda ake kokarin saki ta kafar yanar gizo nan na (utube).
Shugaban hukumar, Dr. Harun Muhammad Sani Ibnu Sina ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwar da jami’in hukumar mai magana da yawun ta, Lawan Ibrahim Fagge ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta yi tir da Allah wadarai da film din mai suna makaranta wanda a ke kokarin sakin sa ta kafar YouTube.
Dr. Harun Ibn Sina ya cigaba da yin caccaka tare da nuna bacin rai, bisa yadda makiya addinin musulunci, na boye da na sarari ke kokarin gurbata tarbiyya da al’adar matasan jihar Kano, maza da yan mata, ta hanyoyi daban-daban.
Dr. Harun Ibn Sina, ya yi amfani da wannan damar inda ya bukaci jama’a musanman matasa da su guji sabawa Allah madaukacin sarki.