fidelitybank

Tsaro: Yawanci daliban bogi ne ke zaune a Danbare – Dr. Idris Rogo

Date:

Shugaban kwamitin tsaro na yankin unguwar Danbare D, a karamar hukumar Kumbotso, Dr. Idris Salisu Rogo, ya ce kusan yankin sun a Danbare yafi kowane waje kalubale a jihar Kano, saboda haka a yanzu haka sun shirya tantance duk wani mutum da zai karbi haya a yankin su.

Dr. Idris Rogo, ya kuma ce a yanzu haka sun hada kai da jami’ar Bayero, domin tantance duk wani dalibi da zai zauna a yankin su.

Dr. Rogo na wannan jawabin ne a lokacin da kungiyar su ta bude sabon ofishin Bijilante, a yankin Danbare.

Ya ce, “Ba za mu yarda Karuwai su tare mana a cikin unguwa ba, saboda haka mun shirya tantance duk wani dalibi a yankin, sakamakon kaso wajen 87 dalibai na bogi ne ke zaune a yankin mu, kuma ba za mu taba yarda da hakan ba, saboda haka mu ka hada hannu da hukumar jami’ar Bayero ta Kano, domin dakile abun”. Inji Dr. Rogo.

A nasa jawabin mai unuguwar yankin, Saifullahi Abba Labaran ya ce,”Mun bude wannan ofishin ne saboda mu dakile duk wasu abubuwan alfasha da a ke gudanarwa a yankin mu, kuma za mu yi aiki tare da ‘yan bijilante, domin samun zaman lafiya mai daurewa a Danbare”.

Da Platinium Post ke tattaunawa da sabon kwamandan yankin Bijilante, Mujitafa Rabilu Muhammad Danbare Dan Inji, ya ce,”Zan yi aiki tsakani na da Allah, saboda na fara aiki ne tun daga matakin kurtu na Bijilante, wanda a yanzu ofishin mu ya zama Unit a tsakiyar gari, za mu yi aiki domin samar da tsaro a Danbare, kuma ba sani ba saboda duk wanda ya yi laifi ko kanina ko dan uwa na za mu ladaftar da su”. Inji Mujitafa.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp