fidelitybank

Ba ruwan Kannywood da sabon fim din da ya yamutsa hazo a Kano – Kwalle

Date:

Shugaban kungiyar masana’antar Kanywood, Alhassan Kwalle, ya barranta masana’antar su a kan wani shirin fim da a yanzu haka a ke tallansa a shafin YouTube.

Alhassan Kwalle ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a kan sabon fim din da a ka far ace-ce-kuce a kan sa.

Alhassan Kwalle ya ce,”Shirin ya sabawa koyarwa ta addinin Musulci da al’adun Hausawa da kuma dokokin masana’antar, domin haka mun barranta kan mu da fim din. Kuma za mu tabbatar da cewa za mu dauki matakan da ya dace na shari’a a kan wanda ya shirya fim din ,duk da mashiryin shirin ba dAn masana’antar mu ba ne.

“Mun yi waya da mashiryin shirin, domin in sanar da shi cewa abun ba dai-dai bane, Amma tun farko ya ce shi fa ba dan Kanywood ba ne, ya shirya shirin ne a karan kansa. Ina da yakinin hukumar tace fina-finan ta jihar Kano ba za ta bar abun sakakaba, yasan za ta dauki matakin da ya dace, domin hana fitar da fim din gudun lalata tarbiyyar al’umma”. Inji Alhassan.

A Jawabinsa shugaban hukumar tace fina-finan Hausa da Dab’I ta Jihar Kano, Isma’ila Na-Abba afakallah, ya ce, ba za mu lamunci irin badalar cikin fina-finan ba, ina da tabbacin hukumar mu za ta nemi mashiryin shirin fim din, domin gurfanar da shi a gaban shari’a. Aikin hukumar ne ta ha na yin fim din da ya sabawa addinin Musulci da al’adun Malam Bahaushe, domin tabbatar da sauke nauyin da Gwamnati ta dora wa hukumar.

Shirin fim din mai suna Makaranta ya dai yamutsa hazo tun bayan sakin tallan kadan daga cikin wani bangaren sa a shafin Youtube.

 

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa ƴar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar Ɗangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp