fidelitybank

Ukraine ta ɗaure Sojan Rasha hukuncin Rai da Rai

Date:

Wata kotu a Kyiv ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani sojan Rasha dan shekaru 21 da laifin kashe farar hular Ukraine, a shari’ar farko ta laifukan yaki da aka gudanar tun bayan mamayar Rasha.

Ana zargin Vadim Shishimarin da harbe Oleksandr Shelipov mai shekaru 62, wani farar hula dan kasar Ukraine a ka a wani kauye da ke yankin Sumy da ke Arewa maso Gabashin kasar a farkon yakin.

“Kotu ta gano cewa Shishimarin yana da laifi, kuma ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai,” in ji alkali Sergiy Agafonov a ranar Litinin, a babban birnin kasar da yaki ya daidaita, in ji Al Jazeera.

“An yi kisan ne da niyya kai tsaye.”

Sojan na Rasha, wanda ya amsa laifinsa, ya shaidawa kotu a makon da ya gabata cewa, ya harbe Shelipov ne, sakamakon matsin lamba daga wani soja a lokacin da suke kokarin ja da baya tare da tserewa zuwa Rasha a cikin wata mota da aka sace a ranar 28 ga Fabrairu, kwana na hudu da mamayar Moscow.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...
X whatsapp