fidelitybank

Tsohon kakakin PDP Olisah Metuh ya nemi yafiya da rokon lafiyar sa

Date:

Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, ya bukaci jama’a da su yi masa addu’a kan halin da yake ciki a halin yanzu na rashin lafiya.

Metuh ya roki jama’a da su yafe masa duk wani abu na bacin rai da ya yi a lokacin da yake kan ganiyarsa, musamman ma kalaman sa na fagen siyasa, tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya.

Olisah Metuh, Ya bayyana cewa, ya samu wasu labarai masu ban tsoro daga likitocinsa, amma ya ce, ya na fatan Allah ya shiga lamarin sa, domin haka ya roki ‘yan Najeriya da su yi masa addu’a.

Metuh na wannan rokon ne a shafukansa na sada zumunta a ranar Juma’a, 21 ga Janairu, 2022, tare da hotonsa a gadon asibiti, bayan an yi masa aikin tiyata.

Ya ce, “A cikin shekara daya an yi min tiyata da yawa, kuma na yi imani da Allah wannan zai zama na karshe. Duk irin fushin da ku ka yi game da furuci na a lokacin da na ke kalamai na na gatse, don Allah ku yi min addu’a”. A cewar Metuh.

latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp