Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF ta ce, tawagar ‘yan wasan Najeriya sune kasar da ta fi ko wacce kasa kokari a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Kamaru.
Wannan ya biyo bayan maki 9 da Super agles ta hada, a duka wasanninta da ta ci na cikin rukuni, inda CAF a wani sakon Twitter da ta wallafa ta ce, rabon da a nuna irin wannan bajinta tun 2010, lokacin da kasar Masar ta yi.
Yanzu dai Najeriya za ta hadu da kasar Tinusia a wasan gaba da za a fara bugawa a ranar Lahadi da karfe 8 na dare agogon Najeriya da Kamaru