Gwamnatin jihar Bayelsa ta tabbatar da kama shanu 44 a cikin Yenagoa, daya daga cikin yankunan da aka haramta kiwon sake.
Kwamitin tabbatar da dokar hana kiwon sake a jihar Bayelsa karkashin kwamishinan noma, David Alagoa, tare da rakiyar jami’an tsaro yayin da suka kwace shanun daga wanda yake tafiya da su.
jaridar Daily Trsut ta rawaito cewa, ba a tafi da mai kiwon ba, kuma ba a kama mai shanun ba, sai dai an tafi da shannun sa bayan tattara su wuri guda.
A watan jiya sai da kwamitin ya kama wasu masu kiwo uku da laifin karya dokar kiwo a fili a jihar Bayelsa.