fidelitybank

TAJBANK ya zama gwarzon bankin musulunci na shekara

Date:

Bankin da baya ta’ammali da kuɗin ruwa, TAJBank ya zama shine gwarzon bankin musulunci na shekara.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa TAJBank ya lashe kyautar ne a wani bikin bada kyaututtuka na shekara ga bankuna da sauran ma’aikatun harkar kuɗaɗe na BAFI 2021, da jairdar BusinessDay ta gudanar.

Wannan kyautar ta zo ne watanni biyu bayan da bankin ya lashe kyautar gwarzon shekara da jaridar Leadership ta gudanar.

Mahukunta a kamfanin BusinessDay, a wata sanarwar da su ka fitar, sun ce TAJBank ya lashe kyautar ne sakamakon ƙir-ƙire na harkar banki da ya ke yi da kuma yadda ya ke daɗaɗawa abokan hulɗarsa.

Sanarwar ta ce” TAJBank ya bada mamaki a harkar banki bayan kafa shi a 2019.

“Yadda bankin ya kawo sauyi mai kyau da kuma ƙirƙire-ƙirƙire da wasu tsare-tsare ma zamani da kuma yadda ya ke bunƙasa harkar kuɗaɗe da daɗaɗawa abokan hulɗa, ya bada mamaki ƙwarai,”

Mahukuntan kuma sun yi hasashen cewa nan da 2021 zuwa 2026, harkar bankin musulunci za ta samu bunƙasa da kaso 15 cikin ɗari.

Jaridar ta kara da cewa in dai TAJBank ya sami lasisin yin harkar banki na ƙasa, to zai ƙara bunƙasa da kashi 65 cikin 100.

Da ya ke bayani bayan bada lambar girman, shugaban TAJBank, Hamid Joɗa ya nuna cewa nasarar ta nuna cewa lallai bankin ma kan hanyarsa ta ƙoƙarin bunƙasa harkar banki maras ruwa a Nijeriya.

 

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp