Shugaban hukumar lafiya ta duniya (W.H.O) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da cewa, tagwayen cutar Korona samfurin Delta da Omicron, na da matukar hadari kamar yadda Tsunami ta ke.
Kalaman Tedros Adhanom Ghebreyesus sun zo ne yayin da Amurka da kasashe a fadin Turai su ka ba da rahoton samun sabbin bular cutar ta Omicron.
Kasar Faransa ta ba da rahoton adadi mafi girma a yau Alhamis cikin kwanaki na biyu da a ka shiga a jere, wanda cutar ta Omicron ta kuma kara fantsama a yankin Turai.
A cikin mutanen da su ka kamu da cutar a kasar Faransa da Turai a rana ta biyu a jere, sun kai mutane 208,000.
A kasar Amurka kuwa ta sanar da cewa, adadin mutane 265,427 su ka kamu a cikin makon da ya gabata, a cewar Johns Hopkins.