fidelitybank

Shirin komawar Kwankwaso APC: Mu na yi masa maraba da zuwa APC – Sanata Babafemi

Date:

Mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya ce, su na yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi’u Kwankwaso marababa zuwa jam’iyyar APC, har idan rahoton ficewar sa ya tabbata.

Akwai rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa Kwankwaso ya koma APC a shafukan sada zumunta.

Yayin da ake ta rade-radin sauya shekar Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa APC, Ojodu ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin “babban mai wayar da kan jama’a, kuma cikakken dan siyasa”.

Ojudu, wanda dan majalisar dattawa ne mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya a jihar Ekiti, ya bayyana hakan a shafin Facebook, inda ya makala hoton Kwankwaso, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kansa.

Ya kara da cewa, “Labarin ya ba ko’ina cewa, shugaban kungiyar Kwakwansiya, mai girma Sanata Rabiu Kwakwanso ya dawo jam’iyyar mu ta APC. Har yanzu ban tabbatar da hakan ba, amma idan gaskiya ne mu na maraba da zuwan shi.

“Haka zalika wannan zai zama mafi kyawu a harkar siyasar sa. Babban mai wayar da kan jama’a, haziki, kuma hazikin dan siyasa, Kwankwaso ne jagoran jama’a masu jan hula. Zai zama babban kari ga yunkurinmu na samar da Najeriya mai girma.”

Sa’o’i kadan bayan jita-jitar sauya shekar tasa, Kwankwaso a wata hira da ya yi da shi ya yi nuni da yiwuwar komawar sa APC.

Da a ka tambaye shi ko zai iya komawa APC, sai ya amsa da cewa, “A siyasa komai na iya yiwuwa a wannan yanayi. Ba ma son kowane maƙiyi na dindindin. Abin da mu ke so abokai ne na dindindin. Ya na da matukar muhimmanci. Muna aiki domin abota.

“Zai ba ka mamaki cewa wasu abokai na da mu ka fara aiki da su shekaru 30 da su ka wuce, yawancinsu suna nan a raye kuma muna tare. Hatta wadanda suka mutu daga shekaru 30 da su ka gabata zuwa yau suna cikin tarihinmu kuma kowace shekara, muna yin abu ɗaya. Domin haka, a cikin 2023, na yi imanin abubuwa da yawa na iya faruwa.” Inji Ojudu.

 

 

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp