fidelitybank

Tsarin Karba-Karba: A mika shugabanci zuwa Kudu a 2023 – Ngige

Date:

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya yi kira da a samar da shugaban kasa daga Kudancin kasar gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Ya kara da cewa, shiyya-shiyya da karba-karba na samar da zaman lafiya, hadin kai, daidaito, ci gaba, amincewa, kishin kasa da kuma tabbatar da cewa babu wata kabila ko wani bangare na kasar da ya mamaye wani.

TheWill ta rawaito cewa, da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a gidan sa da ke garin Alor na jihar Anambra, Ngige ya dage da cewa, akwai yarjejeniya da ba a rubuta ba tsakanin ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa cewa, ya kamata a yi na karba-karba na ofisoshi, kuma a bangaren jam’iyyar PDP an rubuta a cikin kundin tsarin mulkin ta.

Ministan ya ce, ba a rubuta mika mulki karara a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC. Sai dai ya nuna cewa kundin tsarin mulki na 1999 kamar yadda a ka yi wa kwaskwarima ya na goyon bayan karban mukamai na siyasa.

Ya kawo misali da sashe na 14 (3) na kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bayyana karara kan yadda a ke tafiyar da gwamnati a matakin kasa, jihohi da ma kananan hukumomi, ta yadda bai kamata a samu hakikanin ko ra’ayin mamayar wata kabila ko kungiya daya ba na mutanen da suka fito daga wata kabila guda domin samar da kwarin gwiwa da kishin kasa.

A cewar Ngige, “Mulki da kuma rabon ofisoshi na adalci a kowane mataki na sassan tarayya ya samo asali ne daga wannan tanadi. Domin haka a zahiri, dukkanmu mun yarda, daga wannan kundin tsarin mulkin cewa gwamnati a kowane mataki, majalisa, zartaswa har ma da bangaren shari’a, yakamata ya nuna yaduwar kasa ta yadda babu wata kungiya ta musamman ta mamaye sauran.

 “A jam’iyyun siyasa idan kana da shugaban da ya fito daga Kudu, sakataren ya tafi Arewa. Ka na kuma da Mataimakin Shugaban da ya fito daga Arewa. A wasu wuraren kuma suna da mataimakan shugabanni biyu na Arewa da Kudu. Domin haka, duk waɗannan da aka sanya a cikin cikakken kwandon iko, suna nuna muku cewa an gane cewa saboda bambancin mu, muna buƙatar samun dandalin haɗin kai a cikin bambancin.

“Haka kuma a duk lokacin da shugaban kowace jam’iyyar siyasa ya fito daga Kudu, ana yin duk mai yiwuwa dan takarar shugaban kasa ya fito daga Arewa. Hakazalika, akwai wannan shiri da ake yi na tabbatar da cewa mulki ya koma Arewa a duk lokacin da Shugaban kasa daga Kudu ya yi mulki na tsawon shekaru takwas, akasin haka.

“Na ci gaba da yin tsokaci kan abubuwan da suka faru a baya domin wadanda suka shiga siyasa su san tushen wasu tarurrukan. A lokacin da muka kafa jam’iyyar PDP, an amince cewa shugaban kasa ya tafi Kudu. Amma marigayi Abubakar Rimi ya ce a’a, dole ne ya tsaya takara.

“Na tuna Audu Ogbeh, Cif Sunday Awoniyi, Baba Solomon Lar da sauran su, suka kai Rimi wani lungu a gidan Jerry Gana domin tattaunawa da shi, amma har yanzu Rimi ya dage da tsayawa takara. Sunday Awoniyi wanda dukkan mu muke so da mutuntawa ya fara kuka. Awoniyi, cikin kuka, ya ce dagewar da Rimi ya yi ba shine abin da iyayen da suka kafa Nijeriya suka yi hasashe ba ga kasar. Kun san ya kasance sakataren sirri na firimiya na yankin Arewa a lokacin. Mun kasance sababbi a siyasa a lokacin. Ni da Farfesa ABC Nwosu mun kasance muna ɗaukar jakar Alex Ekwueme zuwa taro. Don haka, mu shaidu ne masu rai kan wannan.”

Ya tuna cewa Rimi ya je Jos ne ya dage sai ya tsaya takara amma saboda shiyya-shiyya aka hana shi takara. Ya janye takararsa ne a wurin taron, inda ya bar ‘yan takarar kudancin kasar kamar Cif Olusegun Obasanjo, Alex Ekwueme, Jim Nwobodo da dai sauran su ne kawai suka yi watsi da shi domin neman tikitin PDP.

“Hakazalika a cikin APP, mun sa Ogbonnaya Onu, Olu Falae da hamshakin attajirin nan na Ibadan, Cif Harry Akande, suka yi watsi da shi. Umaru Shinkafi da sauran masu neman Arewa sun sauka. Domin haka, ba labari ba ne a tarihin siyasar Najeriya ka karkata akalar mulkin wuri guda”. Inji Ngige.

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa ƴar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar Ɗangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp