fidelitybank

Rikicin Siyasa: Zaben wakilai a jam’iyar PDP ya bar baya da kura a Zamfara

Date:

Wasu ‘yan bangar siyasa sun mamaye harabar jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, sa’o’i kadan kafin a fara gudanar da zabe wakilai.

Shirin da a ka shirya tun farko na kamfanin man Zaitun dake bayan hukumar alhazai ta jihar, an mayar da shi gidan baki na Command da ke Gusau babban birnin jihar.

A cewar gidan talabijin na Channels, ‘yan barandan sun kai farmaki wurin ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda su ka lalata kayayyakin zabe da fom din tsayawa takara da motoci biyu na ‘yan jam’iyyar tare da kujeru.

Babban Sakataren mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Umar Aminu, ya ce, lamarin ba zai yi wa jam’iyyar barazana ba, ya na mai cewa taron zai gudana kamar yadda a ka tsara.

Ya ce,”Har yanzu ba a san ko su waye ba, kuma na tabbatar da cewa jami’an tsaro za su yi bincike a kai. Ba a dai san ko wace jam’iyya ce ke da alhakin harin da a ka kai a taron jam’iyyar PDP a jihar Arewa maso Yammacin kasar.

Yadda a ka faffasa kujeru tare da kona rumfar zabe a taron PDP

Duk da harin, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Gusau da shugaban riko na jam’iyyar Ambasada Bala Mande sun isa sabon wurin taron.

Zaben wakilan kimanin 1,089 wanda za a gudanar da shi da nufin samar da manyan jami’an PDP wadanda za su gudanar da harkokin jam’iyyar.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp