fidelitybank

Rashe-rashen da a ka yi wa Kano mutane ne jajirtattu – Kungiyar Dattawan Arewa

Date:

Kungiyar Dattawan Arewa (N.E.F) ta yi wa gwamnatin jihar Kano ta’aziyyar rasuwar wasu jiga-jigan ‘ya’yanta ’yan Jihar Kano da su ka koma ga mahalicci.

A yayin da ya ke jagorantar tawagar, shugaban Kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, wanda Wazirin Bauchi Alh.Muhammad Bello Kirfi ya wakilta, ya ce, sun zo gidan gwamnatin Kano ne, domin mika ta’aziyyar rasuwar wasu dattijan jihar da suka rasu kwanan nan.

“Mun zo nan ne, domin ta’aziyyar rasuwar Sarkin Bai, Alh.Muktar Adnan wanda mutum ne mai daraja, da kuma babban likita wanda a ka assasa Wannan kungiyar da shi, Dr. Ibrahim Datti Ahmad da kuma cikakken dan siyasa, Alh.Bashir Othman Tofa.”

“Sarkin Bai uba ne a gare mu, Dr.Ibrahim Datti Ahmad ya kasance mai himma a dukkan ayyukanmu yayin da Alh.Bashir Tofa ya kasance mai hangen nesa da kishin kasa domi son ci gaban al’umma”. inji Ango Abdullahi.

“Wadannan jiga-jigan mutane sun taimaka matuka gaya wajen ci gaban Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya.

Ya kara da cewa suna alhinin rasuwar wadannan manyan mutane wadanda suka bada gudumawa tare da yin tasiri ga ci gaban bil’adama a kasar nan baki daya.

 “Za mu ci gaba da addu’ar Allah Ta’ala ya gafarta musu ya karbi ayyukansu na alheri ya kuma ba su Jannatul Firdaus ya kuma baiwa jihar da iyalansu hakuri jure rashin su”. Inji Ango Abdullahi

Farfesa Ango ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa wannan tarba da a ka yi musu.

Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran mataimakin gGwamna, Hassan Musa fagge wanda ya rabawa manema labarai ya ce da ya ke mayar da Jawabi, gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana jin dadinsa bisa ga ziyarar ta’aziyya da Kungiyar Dattawan Arewa ta kawo wa gwamnati da al’ummar Jihar Kano.

“Hakika mun rasa wasu dattijai wadanda basu da son kansu sun bayar da gudunmawa sosai wajen cigaban jihar Kano da Kasa baki daya”. Inji Dr Gawuna

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp