fidelitybank

Rasha ta gargadi Amurka a kan kasar Ukraine

Date:

Shugaban kasar Russia, Vladimir Putin ya gargadi takwaransa na Amurka, Joe Biden, cewa kakaba sabbin takunkumii kan Ukraine na iya haifar da wargajewar dangantakar da ke a tsakani.

A wata wayar tarho da ya yi da yammacin ranar Alhamis, shugaban na Rasha ya ce, irin wannan takunkumin zai zama “kuskure babba”.

A halin da ake ciki a yanzu, Biden ya shaidawa Putin cewa Amurka da kawayenta za su mayar da martani mai tsauri kan duk wani hari da a ka kaiwa Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, wannan kiran da Rasha ta nema, shi ne karo na biyu da su ka yi irin wannan tattaunawa a wannan watan kuma ya dauki kusan sa’a guda.

Wannan dai shi ne wani yunkuri na baya-bayan nan na kwantar da tarzoma a kan iyakar Gabashin Ukraine da Rasha, inda jami’an Ukraine su ka ce an aike da sojojin Rasha fiye da 100,000.

Wannan ci gaban ya haifar da damuwa a kasashen Yammacin duniya, inda Amurka ta yi wa Putin barazanar kakabawa Putin takunkumi “kamar wanda bai taba gani ba” mudin idan Ukraine ta fuskanci hari.

Sai dai Rasha ta musanta cewa ta na shirin mamaye kasar, kuma ta ce sojojin na can ne domin yin atisaye, kuma ta ce ta na da damar motsa sojojinta cikin walwala a kasarta.

Duk da cewa bangarorin biyu sun yi musayar kashedi a yayin ganawar, mai ba da shawara kan harkokin wajen Rasha, Yuri Ushakov, ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan ganawar Mr Putin ya ji dadin tattaunawar. Ya kara da cewa, hakan ya haifar da “ dankwan alaka mai kyau” domin tattaunawa a nan gaba.

Wani babban jami’in Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ganawar ta su ya kasance mai mahimmanci kuma mai ma’ana.

“Shugaba Biden ya sake nanata cewa, gagarumin ci gaba a cikin wadannan tattaunawa na iya faruwa ne kawai a cikin yanayi na tabarbarewar,” in ji Sakatariyar yada labaran Fadar White House Jen Psaki.

Ta kara da cewa “Ya bayyana karara cewa, Amurka da kawayenta da abokan huldarta za su mayar da martani mai tsauri idan Rasha ta kara mamaye Ukraine.”

 

daily post news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp