Jami’an tsaron kasar Sudan sun harbe mutane hudu a wani samame da a ka yi a fadin kasar a kan zanga-zangar adawa da mulkin soja a ranar 30 ga watan Disamba, kamar yadda ‘yan sandan Sudan suka sanar a ranar Juma’a.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa, jamiāan tsaro sun harba barkonon tsohuwa da gurneti a yayin da masu zanga-zangar suka bi ta birnin Khartoum da garuruwan Omdurman da Bahri dake makwabtaka da fadar shugaban kasa a jiya Alhamis.
A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar sun ce an kashe mutane hudu a Omdurman, sannan masu zanga-zangar 297 da jami’an ‘yan sanda 49 sun jikkata a fadin kasar a zanga-zangar da ta hada dubun dubatar mutane.
Tashar talabijin ta Al Hadath ta rawaito cewa, mai ba da shawara ga shugaban soji, Abdel Fattah Al-Burhan na cewa, sojoji ba za su bari kowa ya jawo kasar cikin rudani ba, kuma ci gaba da zanga-zangar ta kasance kumfar baki ne, domin haka “ba za su bari kowa ya jefa kasar cikin rudani ba. domin cimma mafita ta siyasa.
Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance zagaye na rana 11 na manyan zanga-zangar, tun bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba da ya sa a ka tsige, Abdallah Hamdok, sannan kuma a ka mayar da shi kan karagar mulki. Sai dai masu zanga-zangar dai sun bukaci sojoji da kada su taka rawar gani a cikin gwamnati a lokacin mika mulki a yayin zabe.
Gamayyar Kungiyoyin ‘Yanci da Sauyi ta ce, jami’an tsaro “Sun yi amfani da danniya fiye da kima” a ranar Alhamis tare da yin kira ga al’ummomin yankuna da na kasa da kasa da kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su yi Allah wadai da juyin mulkin.