A jiya ne Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa kawo yanzu an samu bullar cutar guda 45 na Omicron na COVID-19 a kasar nan, ba tare da an samu mace-mace ba.
Darakta-Janar na NCDC, Dr Ifedayo Adetifa, wanda ya bayyana kididdigar Omicron ta Najeriya a wani taron manema labarai, ya ce, sabbin kwayoyin cutar sun kasance a cikin mutanen da ba su da tarihin tafiya, wanda ke nuna cewa kasar ta riga ta fara kamuwa da cutar.
Adetifa ya ce”Mutane Shida na Omicron da a ka gano a baya su na cikin mutanen da ke da tarihin balaguro zuwa Afirka ta Kudu, ya na da kyau ‘yan Najeriya su kiyaye tazarar jiki tare da kaucewa cudanya da duk wanda ke nuna alamun cutar numfashi”.
Ya kara da cewa “Muna dogaro da ku kare kanku da masoyinka daga COVID-19,” inji shi.
Adetifa ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kara bin matakan da za su iya dakile yaduwar Omicron kamar su rage yawan taro, kara nisantar jiki, tsawon lokacin saduwa da kuma yiwuwar rufe wuraren da a ke ganin suna da hadari sosai.
Adetifa ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauki shawarar da kwamitin shugaban kasa ya bayar kan COVID-19 da muhimmanci, ya kara da cewa hakan zai kara habaka tasirin irin wadannan ayyukan.