Gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna damuwa game da ƙaruwar ayyukan ‘yan bindiga masu iƙirarin jihadi a jihar.
Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya faɗa wa BBC Hausa cewa, wannan ne abin da ya fi damun su cikin rahoton tsaro da suka fitar na rubu’in farko na 2022.
Mista Aruwan ya ce “ƴan ta’adda na ba wa mazauna yankunan jihar kyautuka” don jan hankalinsu shiga cikin ƙungiyoyin.
Yayin gabatar da rahoton a yau Alhamis, shi ma Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana damuwa cewa “ƴan ta’adda” na komawa arewa maso yamma daga arewa maso gabas da zimmar haddasa tashin hankali.
Gwamnan ya bayyana cewa babban zaɓen 2023 ka iya gamuwa da cikas idan har ba a ɗauki mataki kan matsalar tsaro ba a jihar.