fidelitybank

Masu buƙata sun yi barazana ga INEC a Ekiti

Date:

Masu bukata ta musamman a jihar Ekiti, sun yi barazanar kai hukumar zabe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan korafin kin tanadar abubuwan da suke bukata, domin shiga zaben gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni.

A cewar Premium Times, shugaban kungiyar masu bukata ta musamman reshen jihar Ekiti, David Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa, matukar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da kara kotu kan take hakkinsu, da dokokin Najeriya suka ba su a matsayin ‘yan kasa.

Mr Anyaele ya kara da cewa, “Duk wani yunkuri na hana ‘ya’yan kungiyarmu kada kuri’a zai sa mu kalubalanci INEC a gaban kuliya domin take dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu kan walwalarmu.”

Ya kara da cewa, kungiyarsu ta damu matuka kan halin tabarbarewar tsaron da ake fuskanta, musamman yadda ‘yan daba ke hana wasu kada kuri’a. Don haka ya bukaci hukumar zaben ta yi aikin hadin gwiwa da ‘yan sanda domin ba su tsaron da ya dace a lokacin zabe

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...
X whatsapp