fidelitybank

Majalisar Dattijai da Wakilai: An bankado badakalar Naira biliyan 8.5

Date:

Ofishin binciken kudi na tarayya ya bankado badakalar Naira biliyan 8.5 a zaurukan majalisar dokoki ta tarayya.

Rahoton binciken kudin ya gano yadda shugabancin zaurukan biyu suka kashe Naira biliyan Uku a majalisar dattawa da wasu biliyan 5.5 a majalisar wakilai a shekarar 2019 ba tare da shaidar kashe kudaden ba.

Mai binciken kudi na tarayya, Aghughu Adolphus, a rahoton sa, ya bankado yadda majalisar dattawa da majalisar wakilai da hukumar kula da harkokin majalisar dokoki ta kasa suka kashe kudaden ba bisa ka’ida ba.

Rahoton da ya gabatar wa Akawun Majalisar a watan Agusta ya ce,  an kashe kudaden ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018 ba tare da cike takardun da suka dace ko rasitin kayan da a ka saya ba.

A shekarar da ta gabata ne kwamitin kudaden gwamnati na majalisar ya kaddamar da bincike kan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya daga 2015 zuwa 2018.

A watan Yunin bana ne kwamitin da rahoton binciken wata shidan da ya gudanar a kan hukumomin.

Da ya ke bayani kan lamarin, shugaban cibiyar bin diddigi da tabbatar da gaskiya a harkokin majalisa (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya ce wannan abin takaici ne kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Sai dai a martaninsa, Akawun Majalisar Tarayya, Austen Adesoro, ya ce abubuwan da ake batu sun shafi shekarar 2019 kuma tuni a ka shawo kansu.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ina nan a PDP na ban gudu ba – Adeleke

Gwamnan jihar Osun, ya musanta rahotonnin da ke cewa...

Tinubu ya isa birnin Rio na Brazil don halartar taron BRICS

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Rio de...

Matakan da muke É—auka kan kisan matafiya a Plateau – Mutfwang

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya ce gwamnatinsa...

Tinubu ya gaji tattalin arziki da ya kusa durkushewa – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya ce...

Har yanzu PDP tana nan da Æ™arfinta – Isa Ashiru

Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da...

An kama ɗan shekara 70 kan zargin kashe ƙanwarsa a Jigawa

Rundunar Æ´ansandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta...

Ahmed Musa za ma sabon shugaban gudanarwar Kano Pillars

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naÉ—a kyaftin...

Netherlands da Jamus sun zargi Rasha da aiki da makamai masu guba a Ukraine

Hukumomin leƙen asirin ƙasashen Netherlands da Jamus sun zargi...

Kotu ta bayar da umarni Majalisa ta dawo da Sanata Natasha

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci...

Sojoji sun hallaka Æ´anbindiga da dama a Plateau

Rundunar sojoji ta ce, ta kashe Æ´anbindiga da dama...

Duk wani tuggun ku Atiku da El-Rufa’i ba za ku iya kayar da Tinubu ba – Bwala

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kokarin da...

Mutuwar Dantata ta girgiza kasa baki daya – Tinubu

Shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu ya bayyana Alhaji Aminu...
X whatsapp