fidelitybank

Jami’an tsaro sun kama masu laifi da muggan makamai

Date:

Rundunar sashen ‘yan sanda na musamman ta kasa, ta ce sun kama wasu da ke zargin masu satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma ‘yan fashi, tare da masu safarar muggan makamai da muggan ƙwayoyi, da satar motoci a iyakokin kasar da kuma fyaɗe da suransu.

Rundunar ta tabbatar da hakan ne a acikin wata sanarwa da ta fitar mai kunshe da hannun ta aka kuma rabawa manema labarai.

Rundunar ‘yan sandan ta ce sun sami nasarar ƙwace bindiga samfurin AK47 guda 18 samfurin GPMG uku, da Ribalba biyu, da karamar bindiga guda, da alburusai 453 da kuma motoci 17 da suka yi fashinsu.

Cikin wadanda aka kama akwai shahararrun ‘yan fashin da ke satar motoci a jihohin Nasarawa da Abuja da Kebbi da Zamfara da Fatakwal.

Motocin da suka sata suna tsallakawa da su iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar domin sayar da su ga wani mutum Alhaji Garba da har yanzu ake nema.

‘Yan sandan kasa da kasa ke aiki da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar, domin gano mutumin da masu taimaka masa, tuni suka gurfanar da su gaban shari’a.

Rundunar ta ce akwai wani matashi mai suna, Dayyabu Muhammad mai shekara 27 dan karamar hukumar Soba da ke jihar Kaduna, da aka samu da bindiga AK47 biyar da alburusai 250 a hannunsa.

BBC ta rawaito cewa, an kama shi ne a samamen da suka kai wa ɓarayin daji a Saminaka da ke jihar Kaduna, kuma bincike ya nuna Dayyabu ne yake kai wa ɓarayin muggan makamai.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp