Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja domin halartar bikin EXPO 2020 Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Laraba.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, wanda PlatinumPost ta samu, ta bayyana cewa, Buhari zai halarci taron bikin EXPO 2020 a Dubia.
Mista Adesina ya bayyana cewa, “EXPO 2020 Dubai, taren mai taken, “Wayar da kan al’umma, domin samun kyakyawar gobe”, ya samar da yanayin da Najeriya za ta shiga cikin ƙasashe sama da 190 domin kulla haɗin gwiwa na gaskiya da ma’ana “domin gina kyakkyawar makoma ga kowa da kowa. Bikin baje kolin zai sake baiwa tawagar Najeriya wata dama ta nuna gagarumin ci gaban da aka samu a fannin tattalin arziki a cikin shekaru shidan da suka gabata a matsayin ginshikin mayar da kasar nan muhimmiyar makoma ta zuba jari kai tsaye daga ketare”.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministocin harkokin waje, Geoffrey Onyeama, masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo, Kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Hajia Zainab Shamsuna Ahmed, Tsaro, Manjo. Janar, Bashir Magashi (mai ritaya), Jirgin sama, Sanata Hadi Sirika, Noma da Raya Karkara, Dr. Mohammad Abubakar da dai sauran tawagar jami’an gwamnati.