fidelitybank

Gwamnati ta kawo karshen kisan gillar da a ke yi wa ‘yan Najeriya – Sheikh Dahiru Bauchi

Date:

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen ayyukan ’yan ta’addar da su ka addabi Najeriya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma bayyana wajibcin gwamnati ta fitar da ’yan Najeriya daga halin tsoron da suke ciki, a lokacin da ya ke jawabi a majalisinsa, inda ya bayyana takaicinsa kan halin rashin tsaron da Najeriya ke ciki.

Ya bayyana cewa, “Ba mu zabe su don mu zama haka ba, ba mu zabe su don mu zama abin tausayi irin wannan ba, ya zama ana kashe mu ba mai kariya ana sayar da mu kamar dabbobi — ana yin abin da aka ga dama da mu — alhali muna da gwamnatoci har guda uku a kanmu; Wannan abin kunya ne, abin dariya ne, abin kuka ne”.

Jawabin malamin na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa sama da mutun 30 a Sabon Birni a Jihar Sokoto, wanda ya haifar da zanga-zanga a Arewacin Najeriya.

’Yan bindiga sun dauki tsawon lokaci suna kashe-kashe da garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa, gami da yi wa mata fyade da kona garuruwa da dukiyoyi da sauran na’uikan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, “Abin da yake wajibi ga gwamnatoci [shi ne] su kula su fitar da mu daga abin da muke ciki na tsoro —kana gidanka kana jin tsoro, kana waje kana jin tsoro, kana tafiya kana jin tsoro, alhali akwai gwamnatoci har guda uku a kanka.”

“Duk muna daura muku nauyi na kuwala da rayukan jama’ar Najeriya da zaman lafiyar Najeriya da walwalar Najeriya; Ina aka ce kasa ko noma ba za a yi ba, to me za a ci?”

Ya yaddada kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi su tashi tsaye, domin yin duk abin da ya dace wajen samar da tsaro da kuma sauke duk nauyin da kundin tsarin mulki ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyi da kuma jin dadin al’ummar kasa. A cewar Aminiya.

 

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp