Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani babban basarake a masarautar Owo da ke jihar Ondo, Elerewe, Tunde Ilori.
Rahotanni na nuni da cewa an kashe Ilori ne a ranar Laraba a lokacin da ya ke dawowa da shi da wasu sarakuna bayan sun je sasanta wani rikicin a yankin.
Haka kuma ‘yan bindigar sun harbe wani basarake wanda har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, kuma a halin yanzu yana samun kulawa a wata cibiyar lafiya da ke garin.
Wasu matasa da su ka fusata a garin da yammacin ranar Laraba sun gudanar da zanga-zanga tare da tare hanya da kona tayoyi a unguwar First Bank da ke Owo.
Gidan talabijin din Channels ya rawaito cewa, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, DSP Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce,”A halin yanzu ‘yan sanda na gudanar da bincike a kan lamarin da nufin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka yi kisan gilla a gaban kuliya”. Inji DSP Funmilayo.