fidelitybank

Garkuwa da Mutane: Jami’ar Abuja ta dauki ‘yan sintiri da ‘yan Banga da mafarauta

Date:

Jami’ar Abuja ta kaddamar da aikin sintiri na awa 24 a cikin harabarta da kewaya ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga, domin dakile ayyukan ’yan bindiga.

Uban Jami’ar Abuja, Modibbo Mohammed, ya ce an dauki matakin ne bayan harin ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu ma’aikata a rukunin gidajensu da ke cikin jami’ar.

Ya ce,“Mun dauki mafarauta da ’yan banga su rika gudanar da sintiri a yankin da babu Katanga, saboda filin jami’ar na da girma sosai,” inji shi.

Amiya ta rawaito cewa, Uban Jami’ar Abuja ya shaida wa taron manyan shugabanni da jami’an gudanarwa da na kungiyoyin jami’ar, cewa su na yin duk mai yiwuwa, domin ganin ba a sake kai hari ba a jami’ar.

Da ya ke magana game da halin da gidajen ma’aikatan jami’ar su ke ciki, ya ce, “Gidajen ma’aikatan mu ba su kai yadda ake bukata ba, har kunya na ke ji game da irin gidajen da ma’aikatanmu ke zaune a ciki. Kwamitin gudanarwar Jami’ar ya yi zama da Ministan Abuja a kan lamarin, kuma ministan ya yi alkawarin daukar mataki a kai, nan ba da jimawa ba. Nan gaba kadan kuma za mu tura wakilanmu zuwa hukumar FERMA, domin ta bayar da muhimmanci wajen gyara hanyoyin da ke cikin jami’ar,” inji Modibo.

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp