Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp ya kyautata zaton cewa dan wasan gaba Mohamed Salah zai rattaba hannu kan sabon kwantaragi a kungiyar.
Dan wasan na Masar ya na jin dadin kakar wasa mai kyau kuma shi ne ya fi zura kwallaye a gasar Premier da kwallaye 13.
Salah, mai shekaru 29, ya koma Liverpool ne a shekarar 2017, kuma kwantiraginsa zai kare ne cikin watanni 18.
A ranar Talata ne Liverpool za ta kara da AC Milan a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Turai, inda tuni kungiyar Liverpool ta tsallake zuwa zagayen gaba.
Salah ya zura kwallo a raga a wasanni shida da Liverpool ta buga a waje a Turai, amma Klopp ba zai bayyana ko dan wasan zai fara wasa a farko ba da AC Milan.