fidelitybank

Siyasa: Atiku zai san matsayin sa na tsayawa takara a sabuwar shekara

Date:

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 21 ga watan Fabrairun 2022, domin yanke hukunci kan ko tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya cancanci tsayawa takarar shugaban Kasa ko a’a.

Mai Shari’a, Inyang Ekwo ne ya sanya ranar da hakan a ranar Litinin, bayan kammala sauraron muhawara tsakanin lauyoyin bangarorin Biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wani kamfani mai zaman kansa mai suna EMA ne ya maka Atikun da jam’iyyar PDP da hukumar zabe (INEC) da kuma Babban Lauyan gwamnatin tarayya a gaban kotun.

Kamfanin dai na kalubalantar cancantar Atikun ta tsayawa takarar shugaban kasa, bisa hujjar cewa ba asalin dan Najeriya ba ne ta nasabar haihuwa.

Ya roki kotun da ta yi la’akari da tande-tanaden sashi na 25 Daya cikin baka (1) da Biyu cikin baka (2) da kuma 131 (a) na kundin tsarin mulki wajen hana shi takarar.

A baya dai gwamnatin jihar Adamawa ta roki kotun da ta saka ta cikin wadanda ake tafka shari’ar da su, inda a ranar 27 ga watan Yulin 2021 kotun ta maince da hakan.

Jihar dai ta shaida wa kotun cewa Atikun ya cancanci tsayawa takara, kuma har ya taba jagorantar Jihar da kuma zama mataimakin shugaban kasa na tsawon shekara Takwas.

To sai dai lauyan masu kara, Oladimeji ya ce ko da ya ke a Najeriya aka haifi Atiku, hakan ba yana nufin shi dan Najeriya ba ne.

A cewarsa, kasancewar an yi kuskure a baya, ba ya nufin a sake maimaita hakan a yanzu.

Daga nan ne Mai Shari’a, Ekwo ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Fabrarirun 2022 domin yanke hukunci.

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...

Tsohon Ministan kuma jigo a PDP ya koma ADC

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda kuma sau uku a...

Trump ya caccaki Elon Musk

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon...

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki shiga jam’iyyar hadaka – Galadima

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...

Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar...

Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu a Najeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana...

Benue da Edo da Bayelsa na fargabar balewar madatsar ruwan Kamaru

Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon...
X whatsapp