fidelitybank

Fim dina ba don mutanen Kano na yi ba – Daraktan fim din Makaranta

Date:

Daraktan fim din ‘Makaranta’ ya ce, bai damu da barazanar da hukumar tace fina-finan jihar Kano ba a kan kama shi da za ta yi.

Hukumar na neman, Aminu Umar Mukhtar ruwa a jallo, inda ta ke zargin sa da lalata tarbiyya da kuma rashin bin ka’ida yayin fitar da tallan fim din.

Fim din ‘Makaranta’ ya nuna abubuwa da dama da mutane da dama suke ganin ba su dace a yi a cikin fim din ba, wadanda su ka hada da madigo da batsa da makamatansu.

Hakan ne ya sa shugaban hukumar tace fina-finan ta Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa, sun aika wa daraktan takardar gayyata a watan jiya, domin ya je gabansu ya yi musu bayani na dalilan da suka sa ya yi fim din ba tare da samun izininsu ba.

A cewarsa, Aminu Umar Mukhtar ya shaida musu cewa zai zo gabansu idan a ka shiga sabuwar shekara, amma bai je ba, lamarin da ya sa su ka fara nemansa ruwa a jallo.

Afakallah ya kara da cewa za su tuhumi daraktan fim din bisa laifukan da su ke ganin ya aikata.

Sai dai Aminu Umar Mukhtar ya ce”Ba Don mutanen Kano na yi fim din ba”.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, Aminu ya kare kansa bisa fitar da tallan fim din, ya na mai cewa,”Ban damu da neman da hukumar tace fina-finan Kano ke yin ba”.

“Na samu labarin cewa hukumar tace fina-finan Kano, ta na nema na. Ban yi ko gezau ba, domin kuwa ban aikata wani laifi ba,” in ji shi.

“Fim din da na yi ba a kan mutanen Kano ko Hausawa na yi ba, na yi amfani da harsuna 17 a cikinsa. Kuma ba a Kano a ka dauki fim din ba, domin haka ban san dalilin da ya sa ya zama abin ce-ce-ku-ce ba. Fim dina ba kawai ya na magana ba ne game da ilimin jima’i ba, ya na kuma nuna illolin kaciyar mata da wayar da kai kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin Hausawa da ma wasu al’ummomi.” A cewar sa.

Daraktan fim din na ‘Makaranta’ ya musanta cewa wasu ne suke daukar nauyin sa, domin ya bata tarbiyyar mutane.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp