Wasu ‘yan bindiga sun kai harin bam a shelkwatar ‘yan sandan karamar hukumar Ideato ta Kudu da ke Dikenafai a jihar Imo.
‘Yan bindigar sun kubutar da dukkan mutanen da a ke tsare da su a wurin.
Dandazon maharan sun banka wa wani bangare na ofishin ‘yan sandan wuta da bama-bamai.
Bama-baman sun lalata ofishin gudanarwa a ofishin jami’an ‘yan sanda na shiyya da kuma ofishin karbar baki.
Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Ideato ta Kudu, Fasto Bede Ikeaka ya bayyana kaduwarsa a kan faruwar lamarin.
Mai magana da rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Michael Abattam, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani ba a kan lamarin. Amm ya yi alkawarin magantuwa ga wakilinmu a nan gaba.
Rahotanni na nuni da cewa, wasu ‘yan banga na yankin sun kama wasu daga cikin wadanda a ke tsare da su.