Shehu Na’Allah Kura, kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano, ya yi murabus.
Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammadu Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Kura ya yi murabus daga kan kujerarsa ta Kwamishinan Ganduje, bayan shugaban ma’aikatan sa Ali Haruna Makoda ya ajiye aikin tare da koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) karkashin jagorancin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Daya daga cikin kwamishinonin tsagin Sanata Ibrahim Shekarau da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ma’aikatar kudi da ci gaban tattalin arziki, Shehu Na’Allah Kura ya yi murabus ya koma wajen ubangidansa.
A cewar Malam Muhammad Garba, an nada Kura a matsayin kwamishinan ma’aikatar ne bisa bukatar Shekarau bayan zaben 2019.