fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Buhari ya umarci sojoji su murkushe ‘yan ta’adda Neja

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sojoji da su mayar da martani mai karfin gaske kan lamarin kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja tare da tabbatar da dabarun da aka sa a gaba ta hanyar amfani da karfi.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi, ya ce, shugaban ya bayar da umarnin ne ga shelkwatar tsaro.

Ya ce”shugaba Buhari a matsayinsa na babban kwamandan sojojin kasar nan ya shirya wani gagarumin farmakin soji a jihar Neja wanda ya ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ragowar ‘yan ta’addan Boko Haram a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar nan”.

A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja, shugaba Buhari ya ce, “Ina so in mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar, sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan. Tsaro hakki ne na kowane memba na al’umma kuma ta hanyar hadin kai da hadin gwiwa da hukumomin tabbatar da doka, zamu iya shawo kan matsalolin a karshe”.

“Gwamnatin tarayya a shirye take ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ‘yan kasa, tabbas za mu shawo kan wannan matsala,” in ji shugaban kasar a cikin sanarwar mai taken “Big military Operation in Niger”.

A ranar Talatar da ta gabata ne ‘yan ta’adda suka mamaye al’umomin karamar hukumar Shiroro ta Neja, inda suka kashe mutane akalla 13 a wani harin da suka kai da rana a Nakundna da Wurukuchi.

Harin na ranar Talata ya zo ne kasa da makwanni biyu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ma’aikata a madatsar ruwan Zungeru, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu ‘yan kasar China uku.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...
X whatsapp