fidelitybank

Cutar Lassa: Mutum 80 sun mutu a Najeriya – NCDC

Date:

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta tabbatar da mutuwar mutane 80 wanda su ka kamu da cutar Zazzabin Lassa.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne a taronta na bayar da rahoto kan barkewar cutar a Abuja, yayin ganawa da manema labarai.

Kawo yanzu an samu mutum 434 da su ka kamu da cutar a fadin Najeriya.

NCDC ta ce, daga watan Janairun 2021 zuwa yanzu, mutum 434 sun kamu da cutar, sannan mutum 80 sun mutu daga jihohi 17 da kananan hukumomi 63 da ke Najeriya,

Ta kuma ce, wannan cutar a Najeriya kamar sauran kasashe ta fi bayyana ne a lokacin sanyi, kamar daga watan Nuwamba zuwa watan Mayu a duk shekara.

Hukumar ta bayyana cewa, Jihar Edo na da mutum 192, Ondo 150, Taraba 21, Ebonyi 17, Bauchi 15, sai Benuwai  mutum 8.

Filato na da mutum 8, yayin da Kaduna ke dauke da mutum 7 da su ka kamu.

Sauran jihohin sun hadar sa Enugu da mutum 5, Nasarawa na da 3,  Kogi na da 3, Cross River na da mutum 1, Imo na da mutum 1, Anambra na da mutum 1, Delta na da mutum 1, sai jihar Abiya mai mutum 1.

 

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp