fidelitybank

Babu maganar zargin Minista ta yi sama da fadi da kudade – Ma’aikatar Kudi

Date:

Ma’aikatar kudi ta kasa, ta musanta zargin cewa, Babban Akantan kasar ya ambaci sunan ministar kudi a zargin da ake masa na halasta kudaden haram da karkatar da kudaden al’umma.

A makon jiya ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar din bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.

Ofishin ministar kudi da tsare-tsaren kasa Zainab Shamsuna Ahmed, sun wallafa a shafinsu na Facebook inda suke musanta zargin cewa babban akantan Najeriya Ahmed Idris, ya shafa wa ministar kashin kaji a zargin da ake masa na almundahanar da ta kai naira biliyan damanin.

Ma’aikatar kudin ta ce an ja hankalinsu game da wani labarin da ta ce na karya ne da aka yada a shafukan sada zumunta, wanda ke cewa babban akantan kasar ya shaidawa wadanda suke masa tambayoyi cewa ministar kudin ta mallaki kadarori a biranen Abuja da Kaduna da kuma Dubai da sunan mijinta.

Sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da labarin saboda acewarsu babu wani zargi da aka yi mata makamancin wannan.

A ranar Litinin 16 ga watan nan ne, hukumar EFCC da ke yaki da hanci da rashawa ta sanar a shafinta na Facebook cewa ta kama babban akantan bisa zarginsa da karkatar da kudade.

Ta ce ya yi hakan ne ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi, wadanda suka kai naira biliyan tamanin, al’amarin da yasa ma’aikatar kudi ta Najeriya, dakatar da Ahmad Idris.

A karshen mako ne kuma, gwamnatin Najeriya ta sanar da nada Anamekwe Nwabuoku a matsayin mukaddashin babban akanta Najeriya.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...
X whatsapp