Hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce ta fara tattaunawa da mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AS Roma, Jose Mourinho, domin maye gurbin Ganoht Rohr a Super Eagles.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta NFF, Melvin Amaju Pinnick ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.
Ya ce ”Super Eagles za ta samu sabon koci nan da mako mai zuwa, abun da ke nufin cewa kocin da ke riko a yanzu ba shi zai jagorance ta zuwa gasar cin kofi nahiyar Afrika ta 2021 ba”
Ya kara da cewa,”Ni da kai na na yi magana da Mourinho kan ko zai karɓi aikin, sannan ministan wasanni, Sunday Dare ma ya yi magana da shi domin jin ko ya na da sha’awar aikin”. Inji Pinnick.