Ƴan bindiga sun sako wasu ɗalibai 30 da wani malami 1 na makarantar Kwalejin Yauri da ke jihar Kebbi.
Sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kebbi kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki ya aike wa manema labarai, ta ce, tuni a ka mika su ga hukumomin lafiya, domin duba lafiyarsu, kuma daga bisani za a sada su da iyayensu.
Shi ma mai bai wa gwamnan jihar shawara kan sha’anin tsaro Garba Rabi’u, ya shaida wa BBC cewa an kubutar da daliban ba tare da an biya kudin fansa ba, ya na mai cewa suna cikin koshin lafiya.
Sai dai ya ce har yanzu akwai sauran daliban da ke hannun ‘yan bindigar, wadanda su ma a ke sa ran kubutar da su nan ba da jimawa ba, a cewar hukumomi.
Rahotanni na nuni da cewa, tun a watan Yunin bara ne dai Ƴan bindigar su ka sace su, wanda a yanzu su ka shaƙi iskar ƴanci.