Majalisar gamayyar jam’iyun siyasa ta kasa ta zabi, shugaban jam’iyar APC, Abdullahi Abbas a matsayin shugaban majalisar reshen jihar Kano.
Da ya ke rantsar da sabbin shugabannin wakilin majalisar na kasa wanda ya jagoranci gabatar da zaben, Nasir Sidi Ali, ya ce, dukkan shugabannin an zabe su ne bayan cika dukkan ka’idojin majalisar.
Ya ce,”Dan takarar jam’iyar APC Abdullahi Abbas shi ne ya yi nasara da kuri’u 13 daga cikin kuri’u 14 da a ka kada a zaben”. In ji Nasir Sidi
A tattaunawar sa da manema labari bayan an rantsar da shi, Abdullahi Abbas ya ce, gamayyar jam’iyun karkashin jagorancinsa zai yi duk mai yuwa, domin ci gaban dimokuradaiyya.
Ya kuma ce,”Duk da cewa kowannen su ya na da jam’iyar sa, amma hakan ba zai hana mu ci gaba da aiki tare da sub a, domin ci gaban majalisar da ma jihar Kano baki da ya”. A cewar Abdullahi Abbas.
An dai zabi Abdullahi abbas na jam’iyar APC a matsayin shugaba yayin da Isa Nuhu Isa ya kasance a matsayin matemakin shugaba sai Nuhu Idris Adam na jam’iyar APM a matsayin sakatare da Abdullahi A Sharif na jam’iyar AAC a matsayin matemakin sakatare.
Sauran shugabannin sun hada da: Ado Muhammad na jami’iyar NRM a matsayin ma’aji da Bello Ado Usaini a matsayin sakataren shirye-shirye, sai sakataren kudi wanda a ka zabi Nasiru Aliko na jami’iyar ADP da Ibrahim Muhammad na jami’iyar APP a matsayin sakataren yada labarai na majalisar da kuma Salisu Umar na jami’iyar YPP a matsayin mai bada shawara a harkokin shari’a.