Wani dan takarar shugaban kasa a karkashin jamâiyyar African Democratic Congress, ADC, Dr Shamsudeen Bashir Lamido, ya ba da tabbacin cewa, Najeriya za ta bunkasa a karkashin gwamnatinsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karbar fom din takara a sakatariyar ADC ta kasa, Abuja.
Lamido ya ce, Najeriya na bukatar wanda ya cancanta, kuma bai kamata a dora muhimmanci kan inda dan takara ya fito ba, sai dai abin da zai iya samarwa kasar. Ya yi alkawarin samar da fili mai kyau ga mata da matasa a cikin gwamnati, tare da jaddada daidaiton jinsi a kowane fanni na rayuwa.