Cibiyar Kula da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta tabbatar da samun sabon nau’in korona mai suna Omicron.
A wata sanarwa da Darakta-Janar na NCDC, Ifedayo Adetifa ya sanyawa hannu a yau Laraba, cibiya ce ta gano nau’in cutar ne mai haɗari a wani gwaji da ta yi.
Ta ƙara da cewa ana zargin waɗanda a ka gwada samfurin nasu sun taho ne daga ƙasar Afirka ta Kudu, inda a nan ne nau’in ya samo asali.
Cibiyar ta ƙara da cewa ta gano sabon nau’in koronan ne a gwaje-gwajen da ta ke yi na matafiya domin daƙile yaɗuwar cutar.
NCDC ta kuma baiyana cewa mutane biyun da a ka samu da sabon nau’in cutar ba su nuna wata alama ta rashin lafiya ba, inda ta ƙara da cewa an fara bibiyar mutanen da su ka yi mu’amala da su.