Fasinjoji fiye da gawarwakin mutane 20 da aka tsamo a cikin ruwa a wani hadarin kwale-kwale da ya kife a kramar hukumar Bagwai.
Jirgin ruwan ya kife ne a kan hanyarsa ta kauyen Badau zuwa garin Bagwai,ciki harda daliban makarantar Madinatu Islamiyya da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.
Daliban da suka rasu, an ce suna kan hanyarsu ta zuwa ne, domin halartar Mauludin da ake gudanarwa duk shekara domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).
A cewar wata majiya a babban asibitin Bagwai, sama da fasinjoji 40 ne lamarin ya rutsa da su ciki harda daliban makarantar Islamiyya.
Majiyar ta kara da cewa kawo yanzu an gano gawarwaki kimanin 20, kuma an ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitin.
Ko a shekarar 2008, fasinjoji 24 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwale ya kife a kauyen Badau a yayin wani bikin aure.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, SFS Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa hukumar kashe gobara na ci gaba da aikin ceto da misalin karfe 9:15 na dare. Kuma sun gano gawarwakin daliban da abin ya shafa da na sauran fasinjoji 20.