fidelitybank

‘Yan sandan Zamfara sun kama matar da take kokarin siyar da dan kishiyarta

Date:

Rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara ta kama wata mata da ake zargi da yunƙurin sayar da yaro ɗan shekara biyu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, kwamishinan ƴan sanda na jihar, Ayuba Elkana ya ce, an kama matar ne tun a ranar 8 ga watan Janairu a yankin Tullukawa da ke Gusau inda ake zargin matar da yunƙurin sayar da ɗan kishiyarta.

Matar wadda asalinta mutumiyar ƙauyen Danyade ce, da ke Maradi a Jamhuriyyar Nijar, an kama ta ne ɗauke da ɗan kishiyarta wadda ta shaida wa jami’an tsaro cewa, ta sato yaron ne daga wajen kishiyarta, domin ita ma ta rama sata da sayar da ɗanta da kishiyarta ta yi a baya.

Amma daga baya ta ƙara shaida wa jami’an tsaro cewa, ta yi yunƙurin sayar da yaron ne, domin samun kuɗin biyan buƙatunta na yau da kullum.

Rundunar ƴan sandan ta ce, za a miƙa wadda ake zargi zuwa ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin zurfafa bincike.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp