‘Yan sandan jihar Kano sun sami nasarar kama wani direban babur mai taya 3 wanda a ke zargi da laifin tserewa da maganin wani mutum da ya dako shi.
Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce”Lamarin ya faru a ranar 3 ga watan da mu ke ciki, lokacin da mai maganin ya dorawa wani direban babur din Mu’azu Idris, maganin ya kai masa unguwar Ja’en, harma sun yi yarjejeniya zai tsaya yayi sallah a masallaci, bayan ya tsaya sallah sai direban ya gudu da maganin”. Inji DSP Kiayawa.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce za ta ci gaba da gudanar da bincike dazarar ta kammala binciken ta za ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda aka sacewa maganin yayi mana karin bayani kan yadda yace direban Adaidaita sahun ya yaudareshi ya tsere masa da kayan maganin nasa.