fidelitybank

‘Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Neja

Date:

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kashe sama da mutune 20 a Galadima Kogo da ke Jihar Neja.

Wasu da suka shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa, ƴan bindigan sun je garin ne da tsakar ranar Asabar misalin ƙarfe biyu na rana kan babura da manyan makamai, inda suka buɗe wuta.

Bayan jama’ar da ƴan bindigar suka kashe akwai da dama waɗanda suka ji raunuka kamar yadda mazauna garin waɗanda suka tsira suka shaida wa BBC.

Rahotanni sun ce, an bindigar sun je ofishin ƴan sa kai sun kuɓutar da ƴan uwansu, sannan suka banka masa wuta tare da wasu motoci.

An ce ƴan bindigar sun shafe aƙalla sa’o’i uku suna buɗe wuta tare da ƙona gidajen jama’a.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na Jihar Neja Emmanuel Umar ya tabbatar da kai harin, cewa har yanzu ba su kammala tantance adadin waɗanda aka kashe ba.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp