fidelitybank

‘Yan bindiga sun bude wuta a kan shugabannin APC na Enugu

Date:

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun yi kutse a wajen wani taron shugabannin jam’iyyar APC a karamar hukumar Enugu ta Kudu tare da bude musu

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar kusan su bakwai sun kashe mutum biyu tare da raunata wasu da dama yayin da suka yi awon gaba da mutum daya daga cikin shugabannin na APC na mazaba ta uku ta unguwar Obeagu Awkunanaw a karamar hukumar Enugu ta Kudu.

Daya daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka kashe shi ne, tsohon shugaban jam’iyyar na karamar hukumar na baya-bayan nan, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban matasa na jan’iyyar na jihar a yanzu, mai suna, Kelvin Ezeoha, a cewar BBC.

Sai dai har kawo wannan lokacin ba a san ko harin na da nasaba da siyasa ba ko kuma hari ne na haramtacciyar kungiyar ‘yan aware ta Biyafara ba, IPOB, wadanda suke kai hare-hare a kan jama’a a yankin Kudu maso Gabas na Najeriya da sunan tabbatar da dokar zama a gida.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, rundunar ‘yan sanda ta jihar ta Enugu ba ta ce komai ba ko fitar da wata sanarwa dangane da harin.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp