fidelitybank

Yajin Aiki: Za mu dauki mataki nan da kwana Biyu – ASUU

Date:

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce za ta dauki matakin da ya dace nan da kwanaki biyu masu zuwa a kan gwamnatin tarayya, saboda gazawar gwamnatin ta cika alkawuran da ta yi mata.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne, ya bayyana haka a tattaunawarsa da Aminiya a ranar Litinin ta wayar tarho.

Shugaban kungiyar ya ce”Za su zartar da hukuncin da ya dace a ranar Talata tare da sanar da dukkanin sauran mambobinta matsayarta game da gwamnatin tarayya”. Inji Farfesa Emmanuel.

Idan ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Oktoba ne ASUU da Ministan Kwadago, Chris Ngige suka gana tare da tattaunawa kan cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta daukar musu.

Daga cikin matsalolin da suka tattauna akwai bukatar yih gyare-gyare a wasu jami’o’in kasar nan da kuma biyan alawus din malamai.

Kazalika, an tattauna wasu alkawura da aka yi wa kungiyar tun a shekarar 2009 da kuma tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS da kungiyar take adawa da shi.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp